YADDA ZA KAYI IDAN MACE BATA KARBI SOYAYYAR KA BA

 YADDA ZA KAYI IDAN MACE BATA KARBI SOYAYYAR KA BA

Hanyoyin da Ake Bi Idan Mace Taqi karban Soyayyar ka.

Karban Soyayya a Wurin mata Babban Ƙalubale ne, Amma yana da kyau Ga Namiji Idan Mace Taƙi Ƙarban Soyayyar shi Ya Iya Danne zuciyar shi cikin Mutunci da Girmamawa. 

Domin Magance irin waɗannan matsaloli mun kawo muku wasu Hanyoyi masu sauƙin bi domin daƙile wannan matsala:

1. Ka Girmama Decision Nata.

Ɗaya daga cikin hanyoyin da zaka bi domin magance Matsala irin wannan shine ka Kasance mai Girmama Hukuncin da tayi akan Soyayyar, domin idan ka tsauwala Za'a iya samun error. Kowa Nada ikon yankewa kanshi abunda yake so Bangaren Soyayya.


YADDA ZA KAYI IDAN MACE BATA KARBI SOYAYYAR KA BA.

Karanta:  YADDA AKE DASAWA MATA SOYAYYA A ZUCIYA

2. Ka Samu Nitsuwa.

Ka Danne xuciyar ka tare da controling na Emotion naka. I mean stay calm. It's Natural kaji Ba daɗi wato Disappointed ko Zafi a zuciyar ka, amma kayi Ƙoƙarin hana zuciyar ka aikata ko furta Mummunan abu. Kada ma ka nuna bakaji daɗi ba. Yayi da ka zama alone sai kayi kukan ka, ka share without anyone noticed.

3. Martaba Kanka.

Ka Kiyaye faɗan maganar da za kaji kunya daga baya, ko kayi danasanin faɗin ta. Ko kayi Attempting ɗaukar fansa. Yadda zaka jure zafin abunda tai maka shine zai nuna cewa kai namiji ne. Ka zama mutum karka bata kanka.

Karanta: LAIFIN MAZA DA MATA ACIKIN SOYAYYA

4. Reflect and Learn

Ka ɗauka Wata dama ka samu domin gyara gaba. Ka duba ko kafun ka tunkareta akwai wani Kuskure da kayi da yakeson gyara. Ka ɗauki Darasi Saboda Gaba domin Ka Ƙarawa ilimin ka Girman yadda zakana Tunkarar mace.

5. Ku Zama Abokai

Idan Har Dama kuna tare kafun hakan ta faru, kuma kuna magana, to ku cigaba da zama Abokai. Ka ɗau wannan nauyin indai zaka iya handling na zama abokai da ita ba tare da wani Matsala ba. A hankali zata sake Fahimtar ka.

Karanta: ABUBUWA 10 DA MATA KE SO A SOYAYYA

Conclusion

Yawancin Maza suna samun kansu a irin wannan halin na ƙin karban Soyayyar daga mace, Kuma sai hakan ya zama da wahala jurewa. Idan har ka tsinci kanka a wannan hali kayi Ƙoƙarin bin waɗannan hanyoyi da muka kawo a sama domin Kwantar da zuciyar ka, dakuma kare Mutuncin kanka.

Post a Comment (0)
Previous Post Next Post