YADDA AKE KIYAYE LAFIYAR IDANU

 ABINCI KALA 7 DAKE ƘARA ƘARFIN IDANU

Kiyayewa dakuma tattalin lafiyar idanu yakan zama babban makama a rayuwar mutum. Sannan babu wani abinci guda ɗaya da Za'a baka guarantee akan yana ƙara lafiyar idanu, saidai Abinci da yawa da  Za'a baka wanda suke da sinadaran da idanu ke buƙata sai kana yawan cin su wanda auke taimakawa wajen kare da kula da lafiyar ido.

Anan Wasu common fruita ne dake da amfani wa idanu:

1. Lemu (Oranges): Lemu Yana ƙunshe da Sinadarai Masu Kyau da Inganci Na Vitamin C, Wato antioxidant wanda suke matukar taimawa wajen kare lafiyar idanu daga Ƙarfin Iskar Oxygen.


2. Gwanda (Papaya): Gwanda Shima nada Sinadaran Vitamin C, E dakuma Beta-carotene, Wanda suke Taimakawa idanu daga zuban ruwa mai ƙarfi. Cin gwanda na taimakawa ido sosai.


3. Strawberry: Shina wani Ɗan Itace ne wato Fruit dake da Vitamin C Sosai a cikin shi, Wanda shima Yana Taimakawa wajen dai daita Lafiyar Hanyoyin Tafiyar jini dake Zuwa wa Idanu.

4. Mangwaro: Mangwaro Source ne babba na Vitamin A dakuma Beta-carotene, Yana da anfani sosai wajen ƙarawa Idanu Lafiyar Aiki sosai, Sannan Yana Kare idanu daga Bushewa.

5. Fiya (Avocado): Fiya Dai wacce muke ci yau da Kullum, Fiya tana Ƙunshe da Sinadaran Lutein, Zeaxanthin, sai Kuma Vitamin E, Wanda ke taimakawa wajen kare idanu daga samun Damuwa ko Lalacewa Bayan Mutum ya Tsufa.

6. Inabi (Grapes): Inabi, Musamman Baƙin Inabi wanda suke da Kalar Red da Purple, Suna Ɗauke da Resveratrol, Sinadari ne dake Tsaftace Hanyoyin jini dake kaiwa zuwa ido wato Blood Vessels.

7. Kankana: Kankana is a good source na Sinadarin Lycopene, Yana Karawa idanu Ƙarfin Gani, Dakuma Kare ido daga Makantar Tsufa. Wato Age-related Mocular degeneration

Tsokaci
Ku Sani Balance diet Yana Da Muhimmanci wajen Inganta Lafiya wato Overall Health, Kuma Harda Lafiyar Idanu. Sannan Yawan Cin waɗannan Fruit ɗin dakuma wasu daga cikin vegetable wato Kayan Lambu Yana Ƙara Lafiyar Jijiyoyin Jiki dakuma Baiwa Jiki damar Rage Proteins.

Post a Comment (0)
Previous Post Next Post