YADDA AKE FARA SOYAYYA DA BUDURWA

YADDA ZAKA FARA SOYAYYA DA WACCE KAKE SOShin kana da wata wacce kake so a zuciyar ka ko wata wacce take sonka amma abun na baka wahala wajen nuna kaima kana so. To ka daure ka karanta wannan gajeren Bayanin da zamuyi domin ka san yadda zaka fara Soyayya. 


YADDA AKE FARA SOYAYYA

 

Da farko yana da kyau kayi tinani mai zurfi akan shin ma wacece wacce kake son nan, ta dace dakai? sannan zaka iya Soyayya da ita ko A'a.


Bayan kayi wannan tinani ka yanke shawari kuma ka ajiye cewa zakayi Soyayya da ita. Abu na gaba shine kayi duba zuwa gareta akan menene yake baka sha'awa da ita ko yake burge ka. Daga nan sai ka jin cewa wannan abun kawai shine kake kallo a zuciyar ka kuma yasa kake son ta.


Sannan sai ka bata Hankalin ka dakuma kulawa, Idan ka bata waɗannan zaka fahimce ta itama zata fahimce ka sosai, kuma zai iya jawo wani ƙarin abunda zaka so agame da ita wanda ma yafi na baya da ka gani.

Yadda ake fara soyayya da budurwa
Ka faɗa mata Abubuwan da kake so da wanda baka so, Saboda tasa me kake so da kuma me ka tsana. Hakan zai bata damar Fahimtar ka itama sosai idan har tana sonka. Duk abunda za tayi to zai zama wanda kake so ne kaima zaka ƙara sonta sosai.


Ka ƙara yawan Lokacin da kake bata, Kana Buƙatar abu biyu Sune Kiran Waya da Kuma Tura Saƙon Text Messages. Sannan ya kasance idan ka kirata itama zata kiraka. Idan ka tura mata Text Itama zata dawo maka dashi. Yawan kira da tura Messages yana saurin saka Shauƙi a zuciyar masoya. Yana sa a tina dakai idan baka kusa.


Ka ƙara da wasanni da tsokana acikin hiran ku, Mata suna son Mutum mai bandariya sosai.

Daga Ƙarshe, Fara Soyayya Yana da Sauƙi Amma yana ɗaukar lokaci da hana aiki kafun ka faɗa duka. Amma ka sani kana Buƙatar shawari mai zurfi kafun ka fara Soyayya da wata mace.


Post a Comment (0)
Previous Post Next Post