HALAYEN MATA TA GARI

HALAYEN MACE TA GARI A GIDAN MIJIN TA




Mata ta gari itace macen da zata so mijin ta ba tare da dalili ba, tasoshi kamar shine kaɗai yafi mata kowa a duniya.


Mata ta Gari itace macen da zata tsaya da mijinta ako wani hali yake ko ya shiga. Ta tsaya a bayan shi sannan ta bashi duk wani goyon baya. Zata sanarwa duniya ƙarfin shi ba Gajiyawar shi ba. Zata saita harshen ta suyi Aiki tare.


Mata ta gari itace zata goyi bayan mijin ta ako me zaiyi na rayuwa. Ba shikaɗai ne zaina baki ƙwarin guiwa ba kema zaki bashi domin ba komai kuɗi yakeyi ba. Zaki iya Taimaka mashi da kuɗi ko Shawari acikin rayuwar shi.Ta Taimaka mishi wajen Sanin Ƙoƙarin shi kuma ta ƙara mishi ƙarfin guiwa akan aikin shi.


Mata ta gari itace wacce ke Girmama maganar mijin ta komin Wahalar abun. Mijin ki shine Keda ƙarfib iko dake fiye da kowa, Ki Girmama shi Sannan Kisan Dalilin da yasa Kika zama Mata Daga Budurwa wanda haka ba abune mai sauƙi ba


Mace ta gari itace macen da ta tsaya akan ƴaƴanta kuma ta naima musu ƙima daraja da mutunci. Ta Kare Ƴaƴan ka Ciki da waje musamman idan akan gaskiyar su ne. Karki Kare su idan Basuda Gaskiya, ki gyara musu kiyi musu faɗa sannan ki Jajirce akan su.


Mace ta gari itace macen da bata kau da kai daga mijin ta dan bashi da shi ko dan ya rasa ko ta halin yaya. Koda yaushe ki ɗauki mijin ki matsayin Mafificin mutum a rayuwar ki. Kimai Addu'a Mai makon guje mishi. Karki raina ƙarfin Namiji.


Mace ta gari itace macen take shirye ta sadaukar da Lokacin ta da Attention ɗinta ga Iyalan ta, Mijinta da Ƴaƴan ta. Ki Baiwa mijin ki Attention, kisan lokutan da yake Buƙatar ki, kisan me zai yi da wanda baya yi. Ki kula da Ƴaƴan ki ki basu lokaci.


Mata ta gari itace macen da take bada lokaci wajen kyautatawa Familin ta. Takan iya sadaukar da Duk abunda ta mallaka don Taimaka wa mijin ta wajen gina Family mai kyau.


Mata ta gari itace macen da bata barin familyn ta su zauna da yunwa Alhalin tana da yadda zata kiyaye faruwar hakan. Karki zama irin matan nan masu son Zuciya wajen son kuɗi kuma da raina abunda mai gida ya kawo. Ki koyi yadda zaki sarrafa kaɗan dake hannu kar kina lissafi da abunda baya Hannu koda naki ne.

Halayen Mata ta gari


Mata ta gari itace macen da take Fahimtar Yanayin mijin ta dana Ƴaƴan ta. Sannan ta biya Buƙatun su.


Mace ta gari itace macen da Bata shiga damuwa ako wani lokaci.


Mace ta gari Bai kamata ta shiga damuwa ako wani time ba, ta zamo mai kwantar da hankali yayin Da ake cikin damuwa.


Mata ta gari itace macen da take ɗaukar magana da Shawarin mijin ta ako wani lokaci. Tana kasa kunne idan mijinta na magana.


Mata ta gari itace macen da bata yiwa mijin ta Tsegumi yayin da baya nan dakuma idan yana nan. Baza'a rasa Matan banza dake yiwa mazajen su Tsegumi ba a cikin anguwa. Ki koyi kame baki da zama a gidan ki.



Waɗannan sune Halayen Mace ta Gari.


Post a Comment (0)
Previous Post Next Post