YADDA ZAKA ZAUNA A ZUCIYAR MACE CIKIN SAUKI

HANYOYI GOMA DA ZAKA MAMAYE ZUCIYAR MACE


Farawa (Preface)

Kamar Yadda kowa ya sani Mata Suna Son Wanda Yake Kyauta ta musu ne, Duk irin yadda kake son mace Matuƙar baka kyautata mata to wataran zaka Haɗu da Fishin Late Comer.

Kamar Yadda Muke so Mata suna nuna mana Soyayyar su A Fili To Suma Mata Suna Son Ana Nuna Musu Soyayya a Fili kuma a Idon Kowa.

Wannan dalili yasa Zamu Kawo muku wasu daga cikin Hanyoyin da zaku bi domin zama daram dam a zuciyar mace batare da wani ya shigo tsakani ba.


1. Kana Yawa  Kiran Ta Da Safiya Kafun ta Karya Koma Ka zamo kaine kake tada ita da Safe, Kana Yawan tambayar ta Yaya Take, Ya Lafiyar jikin ta dana Ƴan Uwanta.

Sannan Sai Ka Baje Kolin Soyayyar ka Da Kalamai masu Daɗi masu ratsa Zuciya Kuna Wanda hankali zai ɗauka.

Bayan Nan Sai Kayi Mata Addu'a Kuma Kace Mata itama tana Muku Addu'a.


2. Kada Ka Yiwa Mace Ƙarya Domin ita ƙarya Ko Ba'a Soyayya ba Tana Lalata komai ta samu.

Idan Kana Son Mace Da Gaske Kuma Soyayyar Gaskiya Ce Ma'ana Soyayyar Aure To Duk Yadda Ranta Zai Baci Ka Faɗa Mata Gaskiya.

Idan Ka Yiwa Mace Ƙarya Daga Baya Ta Gano Abokina RIP Za'a saka akan Hoton ka. Dan Duk yadda kake son Ta Sai Ka Fita A Ranta Musamman idan Ƙaryar Ka Jima Kana Yi Mata.

Mata basa Son Namiji Maƙaryaci. Amma Hakan Fa Ba shine zai Hana Ka Sanin Hanun ka Ba. Ina Ƙara faɗa Kasan Hanun Ka Kawai.

yadda ake soyayya
3. Ka Nunawa Ƴan Uwan ka da Abokan ka Irin Yadda Kake Sonta.

Ita mace Tana son Taga Kana Nuna Ta a Dangi domin Hakan Na Basu Ƙarfin guiwar kasancewa dakai. 

Musamman Kana Yaba Mata a Gaban Abokan Ka, Kana Wasa ta Kana Hura Mata Kai. Hakan Zai sakata farin ciki sannan Kaima zata saka ka cikin farin ciki.

 

4. Ka Tabbatar Kana Biya Mata Duk Wasu Buƙatun ta Wanda Zaka Iya.

Ita mace Idan Tana Sonka Da Gaske Bata tambayar ka kuɗi ko wani abu. Kaine zaka Karanceta sannan Ka Gano Matsalar ta.

Wasu Matan Ko Kayi Musu basa Karba koda da Gaske suna Cikin Matsalar.

Yadda ake musu Shine Zaka Kira Ƙanwarta ko Ƙanin ta Sai ka Bashi Wannan Abun Kace Yaje ya Ajiye mata a gida. 

Daga Baya zata ji daɗin Haka Kuna Zaka Ƙara Shiga Ranta.


5. Idan Mace Tayi Maka Kyauta To Ka Yaba Mata a lokacin Kada ka 6ata Lokaci.

Su Mata ƴan Son a Yaba musu ne. Da zarar mace ta maka kyauta to ka nuna mata kaji daɗin wannan Kyautar, Kyan samu ka Haɗa Mata da Ƴan Kalamai da Zasu nuna Kaji daɗin Kyautar ta.

Sannan Kaima ka Samu Lokaci Kayi Mata Kyautar Bazata.


6. Mata Suna Son Abun dariya Musamman Ma Namiji mai Yawan Bada Dariya. 

Yanxu Yanxu zaka Sace Zuciyar Mace Idan ka iya bada dariya.

Dan Haka Karka Na Tsumewa mace kana Ɗan Tsokanar ta haka kana ɗan Bata dariya koda Tana cikin Baƙin Cikine to zaka rage mata Wannan Baƙin Cikin. Kuma duk lokacin data tina da wannan abun dariyar Zatana tinawa dakai.


7. Inda Hali Kuna Fita Yawon Shaƙatawa, Kuna Zuwa Wajen Cin Abinci Da Wurin Kallon Abubuwan Morewa Idanu domin Hakan Zai saka mace farin ciki Sosai.

Kyan Samu Kuma Kana Riƙe Hannun Ta Kuna Kewayawa Mata Suna Son Haka.


8. Idan Kana Son Mace Ka Fito Fili ka faɗa mata cewa kana Sonta Kuma Ka Yarda Da Ita Sosai, Kuma Ka Nuna Mata Girman Ta A zuciyar ka. 

Sannan Ka Nuna Mata Yadda Kake Girmama Alƙawarin dake tsakanin Ku. Musamman Alƙawarin Aure.


9. Akwai Kalan Wasan Da Mata Basa So. Wajen Hira Kana Fahimtar Yanayin da Mace take ciki dakuma irin wasan da Take so a lokacin dakuma wanda bata so.

Kada ka mata wasa alokacin da kuke magana mai Muhimmanci.


10. Ka Nuna Mata Idan Tana Tare dakai To Batada Wani Matsala. 

Ka Nuna Mata tana cikin Tsaro da Kulawar ka. Ka Nuna Mata yadda kake ji da ita Zakayi Komai akanka.

Hakan Nasa Mace ta sakankance dakai sannan Ta Yarda Dakai kuma Shaƙuwar ku zata Ƙara ƙarfi sosai.


11. Karka Lalata Mata zuciya Domin Duk Lokacin Daka Karya zucomace sau ɗaya, bazata sake yarda dakai ba. Mata suna da Tsork kuma ba ko wace mace bace ake cizon ta sau biyu.Rifewa (Conclusion)

Domin Inganta Soyayyar dake tsakanin Ku Kuna Buƙatar Hanyoyi Sabbi Domin Soyayyar nason ana Bullo da Sabbin Abubuwa masu Ƙayatarwa. Kuma Mata Suna Son Ana Zuwa Musu da Abunda Basa zato ko tsammani.


Post a Comment (0)
Previous Post Next Post