YADDA ZAKA HANA FATAR JIKIN KA TSUFA DA WURI

 YADDA ZAKA HANA FATAR JIKIN KA TSUFA


Engilish: How to prevent Aging?


Farawa (Preface)

Maza da Mata Suna Samun Wani Yanayi da Fatar jikin su take tsufa, hakan na faruwa ne saboda wasu Abubuwa da suke wanda jikin nasu baya son suna ci ko shan waɗannan Sinadaran. Akwai hanyoyin da zaka bi don rabuwa da wannan matsala dake fatar jikin ka.  Kamar su Yanayin Rayuwar ka, Wurin da Kake Zama Kamar Anguwa. Akwai wasu Hanyoyin na Daban Da Zaka Iya Kare kanka Kamar su:


Yadda Zaka Kare Fatar Ka Daga Tsufar Cuta: 


How to prevent skin Aging


1. Ka Kare Fatar Jikin Ka Daga Zafin Rana.

Zaka Iya Kare Fatar Jikin ka Ta Hanyar Shiga Inuwa, Rufe jiki da Kaya ko Amfani da Broad-spectrum, Bawai Ana Nufin Kada Kana shiga rana bane, Amma Ka Kiyaye Jimawa acikin Rana. 

2. Daina Shan Sigari

Idan Kana Shan Sigari to ka daina saboda Shan Sigari Yana Matuƙar ƙara Tsufar fata da wuri. Yana Janyo motsewar fata, Dishewar fata, Ramewar fata. Sannan Yana lalata Huhu da Kyamatar da Jikin Mutum.

3. Gyara cin Abinci

Kana Cin Abinci mai kyau kuma akan Lokaci. Sannan Kana Cin Abinci wanda ya kamata ma'ana Masu Daidaita Lafiya jiki. Ba wai ko wani iri ba. Sannan Kana Cin Kayan lambu Masu Tsafta.

Abincin da Kake ci Yana da Tasiri sosai wajen Ingancin Fatar Jikin Ka.


How Can You Prevent Aging


4. Daina Shan Giya (Alcohol)

Idan Kana Shan Giya to ka Daina Ko Ka Rage, Domin Giya Yana Lalata Fata. Yana Sa Fata Ta Bushe, kuma yasa ta lalace ko ya jawo mata wani ciwo. Kuma yawan shan giya yana saka fatar Tsufa Tun Lokacin Tsufar Mutum Baiyi ba.

5. Rashin Motsa Jiki

Ana Samun Lokacin Motsa Jiki Domin Baiwa Sassan jiki Da Jijiyoyi Samun Isheshshen jini ta yadda zasu Yi aiki dakyau. Kyan samu aje wurin Likita ko Masana motsa jiki domin Samun ƙarfin Guiwa Da Tsarin Lokacin yi.

Motsa Jiki a Lokutan Ƙarshen Mako Masana Suna Faɗa cewa yana Ƙara Lafiyar Jijiyoyin jini wanda hakan nasa Garkuwar jini Lafiya sosai. Wanda hakan zai jawo Gudanar Isheshshen ruwa Zuwa Kan Fata.

6. A Daina Goge Fata da Ƙarfi

Idan Zaka Goge Fatar jikin ka a wurin Wanka, ko Wajen Shafa Mai, ko shafa wani abu daban, a Gujewa Saka Ƙarfi Domin Yin haka na janyi Tsamurewar fata. Ita fatar jiki binta Ake a hankali cikin nitsuwa batare da an ji mata rauni ba domin samu  Lafiya.


How You Can Prevent Aging”


Gargaɗi (Warning)

A Kiyaye Amfani da Kayayyakin Dake Ƙara Farin Fata ko Sheƙi da Sauran su Musamman Masu Ƙona Fata. Yawan Amfani dasu yana janyo Lalacewar fata, Rage Ƙarfin fata, Sannan Yana Cirewa fata Halittun dake Kareta daga Cututtuka.

Rufewa (Conclusion)

A yanxu Mai Karatu ya Fahimci Hanyoyin Da zai kare fatar jikin shi daga Motsewa ko Tsufa Da Wuri. Kuma Muna Fatan Kun Ƙaru sosai. Muna Godiya

Post a Comment

Previous Post Next Post

Contact Form