ILLOLIN CIN NAMA DA YAWA GUDA BIYAR 5

 ILLOLIN DA CIN NAMA MAI YAWA KE JAWOWA AJIKIN MUTUM


Nama na daga cikin Abubuwan da suke da amfani ajikin mutum musamman wajen samar da Sinadarin (Protein) da sauran Nutrients. Kuma abune wanda yake da daɗi a cikin Abincin karyawa. Wasu mutanen suna iya cin abunda bai wuce tsoka ɗaya ko biyu ba na Nama a Rana ɗaya, akwai wasu kuma da suke son cin Nama Sosai Da Yawa musamman acikin Abunda Zasu ci. Koma dai da wani lokaci suke ci, Suna dai cin nama.

Ba Wai cin Nama Laifi bane A'a, amma yawan cin Nama Har yayi yawa ya wuce Ƙa'ida to yana Haifar da Illa. Wannan Shine yake faruwa idan kana cin Abu ɗaya yayi yawa komin Amfanin shi.

Shi Nama, Ga Lafiya baya cutarwa har sai an wuce Ƙa'ida. 

Ga Wasu Muhimman Abubuwan da Cin Nama Yayi Yawa Suke Janyowa ga Jikin Ɗan Adam.:

1. Matsalar Narkewan Abunci (Digestion)

Ɗaya daga Cikin Illan Samun Diet wanda Nama ke kawo shi shine Matsalar Narkewa ta abunci. Saboda diet naka ya rasa Fibre, wanda kuma yana da Muhimmanci ga Lafiyar ka wajen Narka Abinci.

Zaka Na Fama da Rashin Jin daɗin Cikin ka Musamman Jirkicewar Hanji. Kuma zai cigaba da Faruwa Matuƙar Kana cin Nama Fiye da Sauran Abunci.

Daɗin daɗawa, Bama Yana Sa Jiki Kuma Yana Wahalar Narkewa a Ciki. Domin Sanin Adadin Naman da Mutum yakamata ya dinga ci a rana, Ka Tuntubi Likitan ka Domin Samun Cikakken bayani.

Ko Kai da Kanka Ka Rage cin Nama Kamar Yadda kake kullum Tare da Maye Gurbi da Fibre-rich foods Kamar su Hatsi, Shinkafa da Sauran Su.

2. Yana Rage Ƙarfin Kasusuwa (Bones)

Wani Matsalan kuma da yakan iya janyowa ko da zaka na fuskanta bayan kana cin Nama da Yawan da ya wuce ƙima shine Ƙasusuwan jikin ka Zasu rage ƙarfi, Wanda Hakan Na faruwa ne sakamakon Yawan Cin Nama Na Haifar da Raguwar Sinadarin Calcium.

Yawan Hanƙaran Cinadarin Protein wanda Naman Dabbobi ke Ƙunshe dashi yana Haifar da Yawan Sinadarin Acid acikin Jiki, Shikuma yana Ragewa Ƙashi Ƙarfi.

Protein Na Dabbobi Shine Acidic Wato Shine Acid yayi yawa ajikin Mutum, sannan idan yana kewayawa ajiki, Yana Samar da Sulfuric da Phosphoric acids wanda ke buƙatar A Neutralizing nashi. Jiki yakan Neutralizing ɗin wannan acids ɗin wajen fitar da Alkaline da yake cikin Ƙashi, wanda yake Haifar da Rashin Ƙarfin ƙashi.

Ƙarin Bayani, Yawan Protein na Diet Zai Iya Haifar da Raguwar Absorption na Sinadarin Calcium, Sinadarin da aikin shi a cikin ƙashi yake wajen Kare lafiyar ƙashi. Shi Diet dake da High na Protein da kuma Low na Calcium Kan iya Ƙara Yawan Haɗarin Osteoporosis.

Idan Baka Samun Gamsheshshen Abinci mai Sinadarin Calcium da zai na Magance Wanna Gibin na Rashin shi a cikin ƙashi, you might be at risk of Osteoporosis, Wanda Ke Samuwa Domin Rashin Sinadarin Calcium Isheshshe.

Effect of Eatin Too much meat

3. Yawan Ƙarancin Ruwa a Jiki (Dehydration)

Idan Kana cin nama a yawancin lokuta, zaka fara jin ruwan jikin ka na ƙarewa. Dalilin kuwa shine Sinadarin Protein Yana amfani da Ruwa mai yawa wajen Narkewa, kuma Yawan Cin Naman Ka, Yawan Ruwan Da Jikin Ka Zai Buƙata.

Wannan Na Nufin Zakana Fuskantar Samun Dehydration Faster Than Normal. Yawan Shan Ruwa Akai-Akai Zai Taimaka Wajen Rageshi da taƙaita adadin da Rage Yawan Abunda Naman da Kaci Yake Kwasa na Ruwa Kuma Zai Kareka Daga Sarƙewar Ruwa ajiki.

4. Gumi (Meat Sweat or Meat Flush)

Meat Sweat Wani Gumi ne da Mutum zaina Zuba daga jikin shi, Ko Yana Yawan Jin Zafi wato Ɗumi mai saka Gumi Bayan Anci Nama Mai Yawa.

Lallai Duk Wanda yake cin nama mai yawa a lokaci ɗaya zaina yawan Gumi, musamman a dai dai lokacin Mutum ya gama ci. 

Duk da Ana Samun Mutum Yaci Abinci Kuma Yayi Gumi wanna ba matsala bace kuma an saba samu, Amma yawan Gumin da ake yi bayan anci nama da yawa yafi yawan wanda aka saba gani yau da kullum.

Dalilin Faruwar haka kuwa shine Jiki yana aiki da Ƙarfi sosai Wajen Narkar da Nama dakuma Sinadarin Protein Wannan yasa Temperature na Jiki Yake Tashi Alokacin da Hakan ke faruwa, Sai ya Haifar da Yawan Gumi Bayan gama Ci.

Wannan illar ce da ba za'a iya gujewa ba ta cin nama da yawa.

5. Gajiya (Fatigue)

Za Kana jin Gajiya Sosai bayan kaci Abinci mai nama da yawa aciki. Yawan Energy da jiki ke amfani dashi ne wajen narka Nama shiyasa da Abincin ne ya janyo Gajiyar, Wanda haka na kawo Kasala. 

Daga Ƙarshe

Kamar Yadda muka Karanta yanxu, Yawan cin Nama Har ya wuce Ƙima yana da Illa ga Lafiyar jikin Ɗan Adam. Kuma Hakan Yana Ƙara Barazanar kamuwa da cutar Ciwon Zuciya, Da Cutar Kansa Har Ma Da Saka Girman Jiki. Mu Kiyaye!

Post a Comment (0)
Previous Post Next Post