AMFANIN GAUTA GUDA 10
Gauta Yana daga Cikin Ƴaƴan Itatuwa Masu Gina jiki Wanda suke cikin Nightshades Family kuma amfi cin shine a Ƙashashen africa kamar Najeriya, Ghana da Benin Republic. Da Turancin English Ana Ce Mashi "Garden Egg" da Turancin Masu Kimiyar Itatuwa wato Botanical Name Ana ce Mishi "Solanum melongena".
Duk Da Haka Ana sakashi Sahun Kayan Lambu, Za'a iya ce mishi Ɗan Itace Wato Fruit saboda yana Fitowa ne daga Itace Mai Fure kuma a jikin Furen yake fitowa Kuma Yana yin Iri na shukawa.
A Najeriya, Gauta Ba baƙon abu bane Domin abune wanda ake ci yau da kullum. Yorubawa na Kiranshi "Igba" a Najeriya, Igbo Na Kiranshi Ańara, Hausawa na Kiranshi Gauta.
Binciken Likitoti Ya gano Wasu Muhimman Amfani dake tattare da Gauta.
Wasu daga Cikin waɗannan Sun Haɗa da Dietary fibre, iron, copper, potassium, manganese, nasunin acid, chlorogenic acid, folic acid, dakuma da yawa daga cikin Sinadaran antioxidants.
Domin sanin Ma'anonin waɗannan Sinadaran Ayi Bincike.
Acikin Wannan Rubutun, Mun Bankaɗo Muku wasu Muhimman Amfanin Gauta musamman ga Lafiya.
Ingantattun Amfanin Gauta (Garden Egg) Guda 10
Gauta Wanda wasu ke Kiranshi da Eggplants ko Aubergines. Amfanin Gauta ga lafiya ya samu ne daga yawan Sinadaran dake cikin sa wato Nutritions wanda zamu faɗe su yanxu:
1. Yana Rage Ƙiba Sosai
Gauta Musamman Koren shi wato Shuɗi yana daga cikin Abincin da yakamata ka yawaita cinsu idan kana son ka rage ƙiba da Wuri.
Dalili shine wannan ɗan itace yana ƙunshe da Sinadarin Fibre sannan kuma baida Sinadarin Protein da Calories sosai acikin shi wanda sune suke jawo ƙiba, Yawan cinshi yana Bada Himma wajen rage Ƙiba.
Babban Amfanin Cin Ƴaƴan itace irin su Gauta suna gamsar da Mutum da kuma Ƙosharwa, sannan suna rage Sinadarin calories, Ma'ana idan kana cin waɗannan Ƴaƴan itacen, zaka ji ƙarfin jiki da Hanzari Sosai, Kuma Suna Rage Cima Wato Suna Rage Yawan cin abinci.
100 grams na Zallan Gauta yana Ƙunshe da Sinadarai kamar Haka: 4 grams of fiber dakuma 25 calories, wanda masu neman rage ƙiba ke buƙata.
2. Inganta Lafiyar Zuciya
Gauta Kafa ce mai Muhimmanci Dake samar da Sinadarai kamar au Fiber, Potassium, Vitamin B1 (thiamin), Vitamin B6 (niacin) Sai bioflavonoids – Dukkan su suna Ƙara Lafiyar Zuciya matuƙa.
Shi Sinadarai Fibre Yana Taimaka wa wajen rage Barazanar Bugawa ta Zuciya, Heart Attacks, Strokes, Da Atherosclerosis Da Rage matakin Sinadarain "bad" LDL cholesterol, Sannan ya Ƙara Inganta '"Good'" HDL cholesterol a jikin Mutum.
Haka Kuma, Haɗakar Sinadaran potassium da bioflavonoids a cikin Gauta yana taimakawa wajen Rage Iri na cardiovascular system ta hanyar Kula da Yanayin Gudanar jini, wanda hakan shi zai sa zuciya ta ƙara lafiya.
That being said, the Vitamin B1 and B6 contents of Garden Eggs also promote a healthy heart by ensuring that both the nervous and the cardiovascular system are functioning optimally.
3. Inganta Narkewar Abinci
Gauta yana ɗauke da Sinadarin Fibre da kuma Na ruwa, Duka kuma aikin su na Taimakawa wajen Narka Abunci a ciki kuma cikin sauƙi sannan da Kewayawa na Abunci shina yana bada Gudummawa. Muhimmancin Narkewar Abinci da wuri shine yana Taimakawa Garkuwar jiki wacce take tafiyar da Jiki Ya ƙara mata Lafiya. Kuma jikin mutum bazai samu damar yin ƙibar data wuce ƙima.
4. Yana Qarfafa Qashi da Tsoka
Gauta Kafa ce mai Kyau dake samar da Minerals da suka ƙunshi Folate, Potassium, Calcium, iron, Manganese, Vitamin K, Magnesium, vitamin C da Copper, Wanda suke taka muhimmiyar rawa wajen Ƙara ƙarfin Ƙashi da Na jiki.
Ƙarin Bayani, Wasu Masu binkice Sun Sake Tabbatarwa Yawan cin Gauta Yana Rage kamuwa da Ciwon ƙashi da wasu matsaloli da suka shafi na ƙashi.
5. Yana Kare Fata Daga Cutar Cancer.
Bawon Gauta Yana ɗauke da Sinadarin “solasodine rhamnosyl glycosides (SRGs),” wani sinadari ne dake yaƙi da cutar Cancer a cikin jiki.
Yadda ake amfani da Bawon Gauta domin maganin ko Rigakafin anti-skin Cancer, shine ka goga ko ka Shafe jikin ka da Bawon.
6. Yana hana Kamuwa da Cutar Anemia
Anemia cuta ce ta jini ta gama gari wacce ke faruwa lokacin da rashin isassun Ƙwayoyin Jajayen Jini (Red Blood Cells) don jigilar iskar oxygen da ake buƙata zuwa kyallen jikin ku. Yana iya faruwa a sakamakon rashin Sinadaran Iron ko bitamin.
Wasu daga cikin Alamomin Cutar Anemia Sun haɗa da Ciwon kai, Kasala, yawan gajiya, da Yawan Damuwa da Sauran su.
Idan Kana Samun Isheshshen Sinadaran dake cikin Gauta a jikin ka, Cutar Anemia Zata zama tarihi kuma zaka samu kuzari.
7. Yana Dadaita Blood Suger
Gauta Yana da Sinadaran Fibre da Polyphenols wanda suke aiki Hannu da Hannu wajen rage yawan suger na jini. Gauta Yana rage adadin lokacin da sugar yake ɗauka kafun ya narke sannan jiki ya ɗauka. Sannan Yana ƙara "Insulin Secretion".
Idan har haka ta kasance, To Blood Suger naka zai kasance dai dai kuma babu wani cutarwa sai wanda Allah Ya Aiko.
Gauta Yana taimakawa sosai musamman ga masu ciwon suga Saboda Akwai Sinadarin high-fiber diet Sosai.
8. Yana Ƙara Ƙarfin Ƙwaƙwalwa
Gauta Na samar da Sinadaran phytonutrients da Pottassium, Waɗannan Sinadaran suna aikine wajen Inganta aikin Ƙwaƙwalwa da Taimaka mata wajen yin aiki yadda ya kamata dakuma sauran Lafiyar jiki.
Sinadarin Potassium yana Ƙara ƙarfin Fahimta da Basira ta hanyar bawa jini damar kewayawa a cikin Ƙwaƙwalwa, da Ƙara Lafiya tarw da Karw Ƙwaƙwalwa daga shiga damuwa na ciwo.
9. Kariya daga Matsalar Haihuwa.
Amfanin Gauta bai tsaya nan ba harma da Mata masu ciki. Dalili shine saboda Gauta yana ƙunshe da Sinadarai na Nutrition kamar Minerals da Vitamins, wanda Suke Ƙara Lafiyar Juna Biyu.
Misali, Folic acid da gauta ke ɗauke dashi yana taimakawa wajen kare lafiyar yaron dake ciki daga Neural Tube, wanda sun haɗa da Spina bifida, Excephalocele, da Anecephaly.
Illan da ɗa ke samu a ciki shine yana taba Ƙwaƙwalwar yaron, da Spinal cord da sauran wurare masu Muhimmanci. Wannan yasa mata masu ciki ana Basu shawari da suna yawan cin Abubuwan dake ɗauke da Sinadaran Folic acid (kamat su gauta ko yalo) saboda kariya.
10. Garden egg Dakuma Fertility
Gauta Yana Samar da Sinadarai kamar su B-complex vitamins wanda suke zama kamar wani taki ne ga Fatar jiki.
Daga Ƙarshe (Rufewa)
Amfanin Gauta Ko Yalo a Fannin Lafiya yana da yawa ƙwarai. Ana cin su ɗanye kuma suna xuwa ga diet kai tsaye. Yawancin ƴan Najeriya suna yawan cin Gauta da Yalo da Gyaɗa ko su Saka a Cikin Abinci. Duk hanyar daka zaba kaidai ka cigaba da more Amfanin Shi da Romon shi.