ABUBUWAN DAKE SA MATA DA MAZA YAUDARA

DAILILAN DAKE SA MATA DA MAZA YAUDARAN JUNA


Yaudara wani Abune wanda idan ya faru da wani yake jin ciwo sosai, harma takai wasu na iya samun cuta kala kala. Yaudara ba abu ne da Za'a iya Gane shi cikin sauƙi kafun faruwar shi ba, sai ansha wahala wajen bincike ake ganewa.

Wani Shi da Kansa yake jawa kanshi yaudara domin ya aikata wasu kura kurai. Wasu kuma Ƙaddara ce daga Allah Tasa ake yaudarar su ba tare da Laifin su ba kuma basu yi zato ko tsammani ba.

Karanta: YADDA-AKE-RARRASHIN-BUDURWA

Akwai wanda suke yaudara saboda Ɗaukar fansa saboda wani dalili nasu na an yaudare su ko wasu kuma suna yaudara ne dan kawai suyi Nishaɗi wato saboda mugunta.

Dalilan dake saka Yaudara suna da yawa domin kowa da Kalar dalilin shi, Anan Mun tattauna akan wasu daga cikin dalilan dake saka yaudara amma waɗannan ba duk bane:


1. Kwaɗayi

Kwaɗayi wani halittace da Allah ya sakawa dukkan bayin shi na son yin wani abu, ko son Aikata wani abu ko son faruwar wani abu ta wata sigar da Mutum ke so da Sauran su. 

Karanta: YADDA AKE FARA SOYAYYA DA BUDURWA

Kwaɗayi kala kala ne amma wanda muke magana shine Kwaɗayin Kuɗi. Yau idan Kana da kuɗi to kai mata suke yayi. Za'a iya maka duk abunda kake so kuma kake kauna indai kana da kuɗi. 

Wannan dalilin yasa mata gujewa namiji idan baida kuɗi a hannu. Kai ko bakada kuɗi indai kana kashe mata abunda ke hannun ka ko yaya yake to kai take yayi.

Suma mazan yanxu sun fara Cewa sai Ɗiyar mai kuɗi inda Za'a kashe musu kuɗi saboda surukuta.

Abokina idan bakada Sana'a to ka nema, domin mata Masu sonka duk yadda kake basu da yawa a wannan zamani.

Abisa wannan dalili Muke ganin Kwaɗayi na taka Muhimmiyar Rawa wajen Saka Yaudara a zuƙatan Mutane.


Karanta: YADDA AKE RARRASHIN BUDURWA


2. Zugar Ƙawaye/Abokai

Ita dai Zuga wata abace da Jinsin mutane Ke so. A zugaka ka aikata wani abunda baka da niyya ko bakai tsammani ba ko bakasan ma kayi ba.

Zugar Mutane mafi yawa yana Zuwa ne daga bakin Abokai da Ƙawaye, Musamman idan wani abu na shirin faruwa dakai na farin ciki to ana zuga take tashi.

Saidai Zugar wasu na yinta akan abun kirki ko na banza. Wasu su zuga mutum ya aikata Laifi ko ya Gujewa laifi ko ya Rabu da Wani abu da yake so saboda mugunta.

Karanta: AMFANIN AUREN BAZAWARA KO WACCE TA GIRMEKA

Zugar da Muke magana akai Itace Zugar ƙawaye da Abokai wanda suke saka mace ta gujewa saurayinta saboda baida kuɗi ko iko ko kyawu ko dan Taga wani.

Mafi yawanci idan mata na Soyayya da saurayi zugar ƙawaye nasa su guje masa saboda ƙawa tace mata akwai wanda ya fishi koda kuwa Soyayyar gaskiya suke. Domin ƙawaye a wani sigar Suna bada Gudummawa wajen raba kan masoya.

Idan Har zaka Ɗauki Zugar ƙawaye to Kana Ruwa. Shi zugar kawaye gani ake kamar yafi na kowa, idan Ƙawa ta zugaki sai kiji kamar tafi kowa sonki. Hankalin ki da Tinanin ki sune zasu tabbatar miki gaskiya idan har kina su kenan.

Karanta: YADDA AKE MALLAKE USTAZIYA

Mafita shine ki guji Ƙawa da Zata na kawo miki Shubuha akan lamarin rayuwarki. Ki Rungumi Ƙawar da take baki shawari na gari wacce take tayaki kuka da Farin ciki.


Dalilan dake saka yaudara

Karanta: YADDA AKE HIRAR SOYAYYA FARKON HAƊUWA

3. Hassada Don Ana Son Saurayin Ƙawa

Hassada Na Iya Sa Ayi Yaudara. Wata zata ga Saurayin Kawarta taji tana sonshi. Daga nan sai ta fara gujewa wanda take dashi. Acan kuma wajen ƙawar tata, shawari zatana bata gurbatattu kawai saboda ta rabata da Wannan saurayi itakuma tayi Wuff dashi.

4. Rashin Iya Soyayya

Rashin Samun Ilimin Ƙwarewa a Soyayya na iya Janyowa ayi yaudara. 

Kasan Damuwar Abokin Soyayyar ka, kasan me yake so, kasan abunda baya so, sannan ka guje ma abunda baya so, kana aikata abunda yake so.

Kasan hanyoyin da zaka ƙarfafa Soyayyar ka Irin Abubuwa na ban dariya dana Tayar da Shauƙi, Kalaman Soyayya masu Ratsa Zuciya.

Karanta: YADDA ZAKI ZAMA KASAITACCIYAR BUDURWA

Indai Kana Soyayya Kuma Rana zata Fito har ta Faɗi Baka Tankaɗawa Budurwar ka Ko Saurayin ki Kalaman Soyayya ba To Akwai Gyara a Lamarin Soyayyar ku Domin Yin Haka Na Ƙarawa Soyayya ƙarfi da Gujewa Barazanar Yaudara.


5. Rashin Saka Iyaye Cikin Soyayya

Idan Zakayi Soyayya dan Allah To Ka tabbatar ka saka iyayen ka ciki don gudun yaudara. 

Wasu matan suna gujewa maza ne saboda basu da tabbaci cewa wannan saurayi zai Aureta ko A'a. 

Wata kuma gidan su ne Za'a ce ya turo amma sai yaƙi turowa, daga Nan Iyayen ta Zasu hanata kulashi koma su koreshi.

Karanta: YADDA-AKE-YIWA-MAZA-SHAGWABA

6. Rashin Sana'a 

Idan Namiji Baida Sana'a Mata basa bashi Attention dama. Idan kaga mace ta tsaya maka alhalin bakada Sana'a To Ka binciki gaskiyar Soyayyar ta domin idan Ba Sana'a Aure Bazai zauna ba saboda Ita Yunwa batasan Menene Soyayya ba.

Duk Namiji da Baida Sana'a idan Har budurwar shi ta samu wani to Soyayyar su fa Sadai Kariyar Ubangiji Amma sai tayi Rawa da Tangal-Tangal. Kuma wataran saita Guje mishi.

Karanta: ALAMOMIN SOYAYYAR GASKIYA

7. Girman Kai

Mata masu girman Kai Suna Saurin yaudara Kuma Ana Saurin yaudarar su. Idan mace tana da Girman Kai Ko ta amshi Soyayyar ka bazaka ji daɗin yin Soyayya da ita ba domin Ɗagawar ta zatayi yawa. 

Shi girman kai Idan yayi yawa Yana Bata abubuwa da dama sosai. Daga Cikin abunda girman kai ke janyowa Akwai Raini Duk Soyayyar da raini ya ratsata kuwa Bazata haifar da Ɗiya mai ido ba.

Karanta: YADDA AKE MAGANIN MATA

8. Ruwan Ido

Ruwan Ido a Soyayya musamman ga Ɗiya mace matsala ce babba. Domin yana sanya mace taƙi Auruwa akan lokaci. Dalilin hakan kuwa shine Ruwan Ido Na Sanya Yaudara. 

Ruwan Ido nasa Mace Tara samari Da yawa Sama da Guda Ɗaya, Kuma duk bana Aure bane Kawai Ruwan ido ne da yayi yawa sai ta rasa waye zata zaba, Inda daga baya sai kaga duk sun guje mata.

Duk macen da take tara samari kuma anai mata kallon Ƴar iska saboda Macen Kirki An san Bata Tara Samari Da Yawa Haka. 

Duk Saurayin Da ya fahimci Budurwa nada Ruwan Idanu Indai Aure ne ya kawo shi To zai Gujeta daga Nan An shiga Layin Yaudara.

Karanta: YADDA AKE GANE BUDURWA NASON AURE

9. Ƙarya

Ƙarya dai Koda Ba'a Soyayya bama tana zubar da mutunci balle kuma a Soyayya. Yin Ƙarya a Soyayya ya kasu kashi biyu.

Akwai Ƙarya Akan Abunda aka Mallaka misali: Saurayi yazo wurin ki ya ringa ce miki Yana da Mota shi mai kuɗi ne, yana da gidaje Alhalin Baida ko ɗaya daga cikin Abubuwan daya Faɗa miki.

Ƙarya Na Biyu Shine Ƙaryan Soyayya. Zaizo miko ne ta sigar yana sonki Amma kuma Ƙarya yake Yaidarace ta kawo shi. Duk wani Magana mai daɗi da kike son ji ya iyata bazaki taba iya ƙureshi ba saboda ya ƙware sosai.

Da zarar kin Faɗa Tarkon shi sai ya guje miki. 

Mafi yawa Ana Yiwa Mace Ƙarya ne idan Itama Ƴar Ƙaryar Ce.

Karanta: YADDA AKE GANE BUDURWA NASON AURE

10. Zargi

Idan Kuka Cika Zargi Acikin Soyayyar ku To lallai zata tsinka Gadar Soyayyar ku da Kuka Shimfiɗa. Domin zargi a Soyayya Matsala ce babba.

Zargi Shine Yawan Zato Akan Abunda Kake so Alhalin Ba Haka yake ba. Kuma ya Bata Aure Komin daɗewar shi. Yana saka Ƙin Yarda da Juna Dakuma Yawan Faɗa koda yaushe.

Idan Akace Kun samu waɗannan acikin Soyayyar ku to Zata Wargaje, Sai Ɗaya ya Fara Zargin Cewa Ɗayan ya Yaudareshi

Koma Menene Ya Janyo Yaudara Duk Dai Ba Daɗi. Ƴan Uwa mu Kiyaye Yaudara.

Post a Comment (0)
Previous Post Next Post