ABUBUWA GOMA 10 DAKE CUTAR DA DAN ADAM

ABUBUWA GOMA DAKE CUTAR DA JIKIN ƊAN ADAM.


Farawa (Preface)

Idan Aka ce Cutarwa To Abunda zai fara zuwa ga zuciya shine Illa ko Illoli. Akwai wash abubuwa da Muke Aikata su Yau da Kullum wanda kuma a zahiri Ba komai bane. Amma daga Baɗini Suna Cutar damu a 6oye batare da Mun Farga akan lokaci ba.

Wasu Sunsan Hakan na Cutarwa amma wasu Basu Sani ba. Amma idan kuka bamu aron Hankalin ku da Nitsuwar ku zamu tattauna akan su yanxu.

Daga Cikin Abubuwan dake cutar da Jiki Akwai Mani, Atishawa, Bacci, Ƙishirwa, gajiya, Bayan Gida, Yunwa, Fitsari, Hamma, da kumallo.


Zamu Baka Dalila dakuma Yadda ake har su cutar da Mutum Yanxu:


1. Yunwa

Karka Bar Kanka da Yunwa Indai Ba Azumi kake Ba. Domin Barin Ciki da jiki da yunwa Yana Haifar da Cutar Hawan Jini, da ciwon Zuciya da Ciwon Sigar.

Wannan Binciken Masa'ana Ne Ya Tabbatar da Haka. Dan Haka Akwai Cutarwa acikin Barin Cikin ka Da Yunwa.

Akwai wasu Mutanen dake ganin cewa Barin Yunwa har zuwa wani lokaci mai tsawo na kawo cutar Ulcer amma Wannan Hasashe ne kawai na Mutane.

Koma Yaya Dai Barin Yunwa na Lokaci Mai Tsawo Yana Da Cutarwa. Idan Kaji Yunwa Kaci.

Karanta: GASKIYAR BAYANI AKAN FATALWA

2. Ƙishirwa.

Ƙishirwa wa mai tsanani Na sanya jikin mutum Salamcewa wato yaji baida ƙarfi wannan ya samo asaline saboda babu Isheshshen ruwa a jikin mutum Domin duk lokacin da mutum ke jin Ƙishirwa kuma baisha ba har tsawon wani time to ruwan jikin shi zai fara ƙafewa.

Binciken nasana ya tabbar Rashin Shan Ruwa akai Akai Yana Sanya Bushewar Jiki Saboda Ƙishirwa na Jawo Rashin Ruwa a jiki, Inda Rashin Ruwa na jawo Ciwon Kai, Zafin Jiki, da Kasala da Sauran su.

Duk Lokacin Da Kaji Ƙishirwa kasha Ruwa Alaji.

Karanta: AMFANIN AUREN BAZAWARA KO WACCE TA GIRMEKA

3. Bacci

Rashin Samun Isheshshen bacci ko Hana Kai yin Bacci yana Haifar da Chronic Sleep Deprivation wato Suna High Blood Pressure, Heart Attact, Heart Failure ko Stroke, dakuma Rage Ƙarfin Garkuwan Jiki.

Misali: Duk lokacin da Mutum baida Lafiya zakaji likitoci na bashi shawari Yasha Magani ya kwanta yayi bacci. Domin idan Har kana Bacci, To Wasu Part part na jikin Ka Sunfi Yin Aiki Dakyau.

Anason Duk Dare Ka Samu Bacci Na Tsawon Awa 8.

Karanta: YADDA AKE HIRAR SOYAYYA FARKON HAƊUWA

4. Gajiya

Ita gajiya Dai kowa yasan idan Ka tara gajiya To alokacin zaka fara Jin Bacci, sai Ciwon jiki, da Mutuwar jiki. Sannan Zaka na Yawan Gyangyaɗi ako yaushe saboda gajiya. To Duk Lokacin da kaji Bacci Kayi shi.

Idan Ka Gaji ka Huta Domin Jiki Na Buƙatar Hutu.

5. Bayan Gida

Riƙe Bayan Gida Na Tsawon Lokaci Yana Kawo ciwon Mazauni. Yana Illata Magunar Kashi da Kuma Inda Kashin Ke zama.

Sannan Rike Bayan Gida na Jawo Barazanar Kamuwa da Cancer Hanji, Sannan Yana Jawo Matsala wajen Narkewan Abinci. Sanna Da Cutar Ƙoda.

Da wanna Ake Bada Shawari Komin Ƙanƙantar Bayan Gari A cire shi.

Karanta:BANBANCIN BARI DA ZUBEWAR CIKI

6. Fitsari

Rike Fitsari Yana yana Jawo Cutar Ƙoda Sosai, Sannan Yana Kashe Gaban Ɗa Namiji Kuma Yana Kawo Infection Da Ciwon Mara saboda Yana Haifar da Bacteria. 

Sannan Riƙe Fitsari na Tsawon lokaci yana ragewa Mafitsara ƙarfin riƙe Fitsari.

7. Hamma

Masana Kimiya Sun bada Shawari kada Mutun yana Riƙe Hamma Domin Rashin Riƙe Hamma yana Taimakawa Lafiya.

8. Atishawa

Yayin da Atishawa tazo kayita. Bincike na masana ya tabbatar cewa Yin Atishawa na buɗe ƙofofin jini Wato Blood Vassel. Sannan Riƙe Atishawa Yana Toshe su. Kuma Riƙe Atishawa Yana Rufe Drums na Kunnuwa wato yana kawo matsala ga Jin Mutum. 

Abubuwan dake cutar da Mutum

Karanta: YADDA-AKE-RAGE-SHA'AWA


9. Kumallo

Iyaye da Kakanni Sun tafi akan cewa Rashin Cin Abincin safe Yana Janyo Rashin Ƙoshi a Gabaɗaya Wannan Wuni. Domin Sun Yarda Cewa Indai Ka Ƙoshi da Safe Yadda ya kamata to Zaka Jima Baka jo yunwa ba.

10. Maniyi (Sparm)

Rashib Fitar da Maniyi Yana Janwo Mental Problem Inji Masana Kimiya. Harma Wani Bincike ya Tabbatar cewa Wani kaso Na Nau'in Mahaukata Yafi samuwa a wurin marassa Aure.

Zaman Maniyi a Jikin Mutum Yana Janyo Ramewar jiki Da Sanya Damuwa a Ƙwaƙwalwa.

Gayu ayi Aure Domin Fitar da Maniyi Ta kowace Hanya Haramun Ne.

Karanta: ILLOLIN CIN NAMA DA YAWA, MUSAMMAM JAN NAMA

Rufewa (Conclusion)

Idan Kun Fahimci Abubuwan da Muka Tattauna Zaku Fahimci Cewa Duk Abubuwan nan Guda Goma Suna da Alaƙa ta wata sigar. Su Riƙe Waɗannan Abubuwa Goma 10 Matsala Ce Ga Rayuwar Ɗan Adam. Akiyayr Ƴan Uwa.

Post a Comment (0)
Previous Post Next Post