KALAMAN SOYAYYA GUDA 40

 KALAMAN SOYAYYA SABABBI GUDA 40

 40 Romantic Love Text Messages


40 Love Text Messages ne da Muka shirya muku domin Nishaɗi da Jindaɗin Masoyan ku. Wato Kalaman So Ga Budurwa, kalaman yabon budurwa, ko yadda ake tsara budurwa.


Ga Mata, Zaku Iya Aikawa Samarin ku wannan saƙo Domin Ƙarfafa Soyayyar ku ta hanyar canja Manuniyar Mace izuwa na miki. 

Misali: ina Sonki: Zuwa Ina Sonka!

1. Saƙon Gaisuwa ta musamman zuwa ga Kyakkawa kuma mai ban ƙawar Budurwata. Farin ciki da murna sun tabbata ga wanda ke tare dake, Tinanin Ganin Ɗauke baƙin Ciki yake. Ina fatan Wannar ranar ta kasance Kyakkawa.

2. Lallai na kasance mai Sa'ar samun mace kamar ki. Kin fiddani daga cikin duhun dare kuma kin sani murna da farin cikin da yazo daga gareki. Kawai ina sonki ne Daga Zuciya ta.

3. Saboda ke, ina cikin farin ciki da ban taba sanin shi ba, kuma bansan dashi bama. Kasancewa dake shine gaskiyar Mafarkina , Nagode da kika zama bangaren rayuwata.

4. A Tsakanin Zuciyata da Tinani na Akwai wata kujera wacce nakeson baiwa macen da zata iya sharemin hawayena, ta bani farin ciki, tayi renon ƴaƴana, Ta kula dani. Na miki Alƙawarin mallaka miki wannan Kujerar.

5. Kece kika fara maida tinanina me Ma'ana, koda zan wuni cikin damuwa, nasan idan na kasance dake to kafun yammaci na manta da damuwa. Kece mafi girman kyauta dana samu a rayuwata.

6. Inason Murmushin ki, ina son jin muryarki, komai naki na burgeni, zanso nayi shekara ɗari 100 tare dage cikin Soyayya da Ƙaunar Juna, Ina Sonki Matata!

7. Idan Haske ya haskaka dare gari ne yake wayewa, idan Soyayyar ki ta motsa acikin xuciyata, Farin ciki ne yake mamayeta saboda tasan Za kiyi mata mulkin adalci. Masoyiyata Ina Sonki!

8. Irin Soyayyar da Kike mini baza'a taba samu ba a ko ina a Faɗin Duniya. Ina sonki fiye da Kowa acikin wannan duniyar. Addu'a ta Kullum shine Allah ya bani ikon nuna miki Soyayya irin wacce kike min watarana na zama irin namijin da kike so. My dear love!

9. Ban taba haɗuwa da mace irin ki ba. Ke wata abar al'ajabi ce dake faruwa a rayuwata. Soyayyar ki wata damace ta mulki dana samu wacce bazanyi wasa da ita ba. Nayi sa'ar samun ki a rayuwata.

10. Na samu kalar budurwar da zuciyata ke fatan mallaka, ina fatan zaki kasance inuwa agareni mai sanyi.


ƘAYATATTUN SAƘONNIN SOYAYYA

11. Darajar ki tafi ta Lu'u-lu'u, hasken ki tamkar Ruwan sha ne da nake buƙata yayin Ƙishirwa, ban taba nitanin irin Soyayyar ki zai kasance ba, amma kin chanja rayuwata. 

12. Ranar dana fara ganin ki, na kasa fitar dake a tinanina. Zuciyata ta narke da Begen ki. Kece Amaryar Ruhina. Ina Miki Soyayya Irin wacce ni kaɗai zan Iya miki ita.

13. Burina na Kasance dake koda yaushe. Inda zan kasance ako wani yammaci akan tafin hannun ki, to nifa na gama samun duniya. Zan kwantar da Hankali na, na sanya zuciyata sauraran tattausan lafuzan dake fitowa daga Labban bakin ki.

14. Zaki zama zabina ne idan Har kika soni, nikuma zan mai dake Sarauniya ta idan har na sameki. Rayuwata taki ce Habibina!

15. Nayi Fatan Ace kina kusa dani yanxu, da zan Rungumeki, Nayi Miki Kiss. Saidai kinyi Nisa dani, Amma zuciyata na tare dake!

16. Ke kamar walkiya kike bakya zuwa sai ana ruwa, Kin zama hadari mai bani ruwa yayin da na faɗa damuwar Ƙishirwa. Nifa ko damuwa bata zuwa inda nake yanxu saboda inada ke! 

17. Tun ranar dana haɗu dake, Na rasa duk wani dalilin yin baƙin ciki, gaskiya ke ta dabance. Bazan saurara ba wajen nuna miki Qauna My Soul!

18. Ina son ganin ki aduk lokacin dana shiga damuwa ne saboda kalaman bakin ki na ɗebe min kewa. Tazarar dake tsaknin mu itace matsala. Amma daga cikin xuciyata Kullum gado ɗaya muke kwana. Sahibata Ina Sonki.

19. Ke tawa ce ni kaɗai, ina martaba ki. Domin kina mulkin zuciyata. Samun ki nasara ce da ban taba yi ba a rayuwata. Ina son ka kashe lokaci na koda yaushe dake. Have a Amazing Day!

20. Na kasa nistuwa na kasa jurewa na kasa ganin kowa sai ke, kece farin cikina kece dariyata, kece Murmushi na. Burina ki zamo farin cikina.


Text Message for Lovers


21. Tun ranar da nai kicibis dake, nasan kece zako samu lambar girmamawa daga zuciyata. Duk ranar da muke tare, ji nake nafi ko wani namiji Sa'a. Zuciyata ta Maƙalewa kalaman ki. Bazan iya rayuwa babu ke ba.

22. Na tsani duk wani lokacin da bama tare kuma muna buƙatar juna. Lokacin da Nake so a rayuwar Soyayyar mu shine lokacin da muke tare. Bazan taba nisa dake ba my Life!

23. Na baki zuciyata, yanxu ya rage naki. Ki ajiye ko ki jefar, amma zuciyata zata kasance mallakin ki. Kin nuna mini menene Soyayyar gaskiya, kuma naji daɗin shigowar ki rayuwa ta. Have a Great day!

24. Murmushin ki na ƙayatar da zuciyata, Farin cikin ki adone da nake taƙama na sanyaki aciki. Yau kece Siterin Ruhina ki juyani yadda kika so.

25. Ki kasance dani cikin daɗi ko wuya, nikuma zan hana duk wata damuwa kusantar taki rayuwar. Alkawarina ne!

26. Saƙon murmushi zuwa ga wacce zuciyata keda burin mallaka akoda yaushe, saƙon farin ciki nake isarwa zuwa ga wacce yake da isa mafi isa daga cikin masu isa afadar zuciyata, me kyau nakasa misalta irin yanda nakejin sonki acikin jijiyar dake aika jini dukkan sassan jikinah,

 a kowane lokaci da kowani yanayi kece abar tinanin kwakwalwata,

27. Me kyau soyayarki daɗa ƙaruwa take akowanni sa'a na agogo, kin kasance wani bangare daga cikin jikina wanda yafi komai muhimmanci shiyasa baki da tamka ackinta, na mallaka miki zuciyata da dukkan soyayyata domin kece wacce kikapi chanchanta dana mallakawa, ina mutukar alfahari dake, kuma ina fatan zaki kuladani kuma kikulaman da kanki sarauniyata,  

28. Hubbina kisanar da zuciyar ki cewa ina gaisheta, sannan ki sanar da ita cewa a ko yaushe bani da burin da yawuce na ƙosar da ita da kalamai waɗanda zasu ratsa duk jiki da jinin jikin ki. domin ki samu tabbaci kuma kiji a jikin ki cewa kina dani a duniyar masoya abar kaunata, zuciyata takamu da kaunarki matuka masoyiyata. 

29. Zan iya mallaka miki gangar jikina, da Ruhina, Da Zuciyata, Amma Rayuwata Dama takice. Kece mace ta biyu mafi girman Alfarma a rayuwa ta. Bazan taba Mantawa dake ba.

30. Koda yaushe kina tsagina, dan haka bazan iya biyanki ba. Idan bakya nan ina jin ciwo sosai. Abunda nake iyawa kawai shine na fara tinanin ki sannan na jira dawowarki. Ina sonki kuna bazan gaji da faɗa ba har sai bana numfashi.

31. Babu wacce ta isa ta dagula Soyayyar ki, domin niɗin mallaki ne gareki ke kaɗai. Idan kina kusa dani fatar jikina motsawa take. Wani shauƙin sai Kin Mini wannan kallon!

32. Gonar da nake nomawa acikin zuciyata tayi tsiron Soyayyar ki, Gashi har na fara ganin furenni tako ina suna zana mini sunan ki!

33. Ba ai macen da zata zo inda nake domin ƙwace miki ni ba, duk Soyayyar da zanyo bayan taki zata biyo. Duk Soyayyar da wata zata nunamin saidai tayi kwaikwayo amma kin ci gari kuma an baki naɗin Sarautar Sarauniya.

34. Da zan iya San'ar zane, Bazan iya zana hoton da ba naki ba. Ko wani lokaci na tina ki a zuciyata hoton kine yake mini gizo a idanu na. Na zauce a Soyayyar ki!

35. Kin cancanci Soyayya ta, duk wani gurbi dake Maƙale a birnin xuciyata kin cike shi da Soyayyar ki, Sahibata Anya zaki bari Soyayyar ki ta barni nashaƙi iskar Soyayyar watan ki kuwa?


Kalaman love


36. Duk lokacin da Kike cikin damuwa saina faɗa damuwar da ta ninka taki domin wacce take fiddani a damuwa da shiga damuwa. Nayi Alƙawarin wanzar da farin ciki a xuciyar ki iya Ƙarfina.

37. Kece sanadin farin cikina, Amanarki farilla ce na rike, domin kina ɗauke da Duk wani dalili da zaisa na faranta miki ruhi. Kuma na kori baƙin ciki tare da maye gurbi da Murmushi.

38. Kece Alƙiblata a Soyayya. Ina fatan Rayuwar mu tare ta kasance mafi nasara akan ta baya. A wannan lokaci naso ace kece a gefe na yayin da Muke hirar farin ciki da Soyayya.

39. Idan zan rubuta yadda nake Qaunar ki, Za'a karaɗe faɗin wannan duniyar Ba'a samu takardun da zasu ɗauka ba saidai Maleji. Have a Great Evening!

40. Kece mafi ƙololuwa a zuciyata kuma dalilin da yasa ruhina ke rera waƙar begen ki. Saboda ina da Gata a rayuwa yanxu. Ina Ƙaunarki.

Post a Comment (0)
Previous Post Next Post